Tauraron dan kwallon kafar Brazil da Barcelona,  Ronaldinho a jiya,Asabar ne ya cika shekaru 40 saidai ya cika wadannan shekarunne a gidan yari.

 

Ronaldinho na tsare kusan sati 2 kenan a gidan yarin kasar Paraguay shi da dan uwansa saboda zarginsu da shiga kasar da fasfon bogi sannan ana tsammanin idan kotu ta sameshi da laifi zai iya kaiwa tsawon watanni 6 a gidan yarin.

 

Saidai duk da yana tsarene, Ronaldinho ya samu dan kwarya-kwaryar bikin murnar zagayowar ranar haihuwar tashi inda har gashin nama aka masa.

Ronaldinho mayen murmushi da Dariyane koda a filin kwallo da wuya kaga abinda zai bata masa rai.

 

Wani Rahoton ESPN ya bayyana cewa, Ronaldinho yayi kokarin shiga cikin wanda ake tsare dasu tare dan ya zama abokinsu kuma hakan yayi tasiri dan kuwa da dama suna sonsa, dan yana da farin jini sosai, sukan buga kwallo tare, harma da masu tsaron gidan yarin, sukan bashi riguna da huluna da litattafai dan ya musu rubutu akai.

 

Rahoton yace an baiwa Ronaldinho da dan uwansa kulawa ta musamman inda aka basu dakuna kowanne da nasa kuma suna da na’urar sanyaya daki da talabijin a ciki saidai suna amfani da bandaki daya da sauran mazauna gidan yarin.

 

Ronaldinho na amfani da waya, har Cattin yana yi sannan a kullun sai ya gaisa da mahaifiyarsa, yakan nuna son magana da mahaifiyarsa sosai.© hutudole

Post a comment

 
Top