Sojojin Najeriya da ke yaki da masu satar mutane a jihohin Zamfara da Katsina sun ba da rahoton cewa sun kawar da wasu ‘yan bindiga guda 26 a bata kashin da sukai da yan bindigar, inda suka samu nasarar kubutar da mutane tara da’ yan bangar suka sace a sansanoninsu.

Birgediya Janar Bernard Onyeuko, Daraktan Watsa Labarai na Tsaro, shine ya bayyana hakan, jiya, a Abuja.

A yayin aikin, an gano bindigogin AK 47 guda 4, bindiga 2 da bindigogi masu babura 3, harsashi 17 na bindigogin mm 7.62 na AK 47 da babur daya.

A cewarsa, tsakanin Alhamis 18 da Juma’a 19 ga Maris, “Runduna ta Operation Hadarin Daji da ke aiki da sahihan bayanan sirri sun gano tare da lalata wasu sansanonin ‘yan fashi 2 a garuruwan Bindim da Koli na karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

Haka zalika sojojin Operation Hadarin Daji, yayin da suke sintiri a Gando, sun kubutar da maza 7 da mata biyu da yan fashin suka sace.

An mika wadanda abin ya shafa ga iyalansu© Abubakar Saddiq

Post a comment

 
Top