Jihar Oyo ta bayyana samun mutum na farko da ya kamu da cutar Coronavirus/COVID-19.

 

Gwamnan jihar, Seyi Makinde ne ya tabbatar da hakan inda yace gwajin da akawa wani mutum da ake zargin na dauke da cutar ya bayyana kuma an gano yana dauke da cutar.

 

Ranar Asabar, 21 ne gwajin ya bayyana, kamar yanda gwamnan ya tabbatar.

 

Gwamnan ya fitar da sanarwar a yau, Lahadi.

 

 © hutudole

Post a comment

 
Top