Tsohon Shugaban Real Madrid ya mutu ranar sati bayan ya kamu da cutar corona virus/Covid-19. Sanz mai shekaru 76 ya kasance shugaban Madrid na tsawon shekaru biyar tun daga shekara ta 1995-2000.

Kuma a lokacin shi ne Madrid taci champions lig har sau biyu. Kuma ya siya manyan yan wasa kamar su Roberto Carlos,Clarence Seedorf da Davor Suker. Ya rasa shugabancin shi a zaben da sukayi na shekara ta 2000 ayayin da Florentino Perez ya cigaba da shugabancin Madrid.
Yaron shi Lorenzo Sanz Duran a shafin shi na twitter yace, babana ya mutu. Kuma ya kasance a yaruwar sa ba abun da yake so kamar iyalin shi da Real Madrid.
Yaron shi Fernando maishekaru 46, ya yi wasa a Real Madrid tun daga shekara ta 1996-1999, sai ya koma Malaga na tsawon shekaru 7 daga nan sai ya daina wasan kwallo.


© Ahmad A

Post a comment

 
Top