CORONA VIRUS: Sanarwa Daga Gwamnatin Jihar Kaduna

 

A yayin da gwamnatin jihar Kaduna ta kammala shiri tare da daukan matakan tukarar iftila’in cutar Corona Virus wadda ta shigo Najeriya kuma ta ke ci gaba da yaɗuwa duk da cewa gwamnatoci na iya bakin kokarin su don ganin sun dakile yaduwar ta.

 

Ma’aikatar lafiya ta jihar na sanar da al’umma mazauna Kaduna da su kwantar da hankalin su sannan su yi ƙoƙarin ƙiran ɗaya daga ciki wadannan layuka 08025088304,
08032401473,
08035871662
Ko

08037808191 nan take da zaran sun san wani da ke da alamun kamuwa da wannan cuta ta hanyar yin bushashen Tari, Zazzabi, Gajiya ko yin numfashi da ƙyar (Numfashi sama-sama) domin daukan mataki cikin gaggawa.© hutudole

Post a comment

 
Top