Jaruman sojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga 26 a jihohin Zamfara da Katsina inda suka kwato makamai da kubutar da wasu mutane da aka yi garkuwa dasu.

 

Jami’an tsaron sun shiga kananan hukumomin Jibia dake Katsina da kuma Maru dake Zamfara bayan samun Rahoton cewa wasu ‘yan bindiga sun tasa wasu dabbobin jama’a zasu gudu dasu.

 

A Jibia, jami’an sojin sun tare maharanne a garuruwan Gurbin Magarya, Kwari, da garin gado, inda suka kashe 24 daga cikin maharan sannan suka kwace bindigar AK47 guda 4 da sauran wasu makamai, kamar yanda sanarwar Sojin ta Ranar Asabar ta bayyanar.

 

A Maru kuwa an tare ‘yan bindigar ne a Garuruwan Bindim da Koli inda jami’an soji suka kashe guda 2 tare kwato harsasai da dama.

 

Daraktan watsa labarai na sojin, Birgediya Janar Benard Onyeukor ya bayyana cewa sojin sun kwato mutanen da aka yi garkuwa dasu guda 9, 7 maza, 2 mata, sannan sun kwato Shanu 42 da kuma Tumaki 38 inda suka ci gaba da kula da yankin.

 

 © hutudole

Post a comment

 
Top