A jawabin da Gwamnan Jihar Akwa-Ibom, Emmanuel Udom ya yi was mutanen jihar, ya ce gwamnati ba zata rufe makarantun jihar ba tunda babu rahoton cutar a jihar.

 

 

” Bari in sanar muku yau cewa babu rahoton cutar coronavirus a wannan jiha. Saboda haka ba zamu rufe makarantun mu ba, amma za mu maida hankali waje ganin cutar bata shigo mana ba.

 

 

Jihar Akwa-Ibom ta kakkafa wurare domin ko da za a samu wani da ya kamu da cutar a jihar. Mun samar da motocin daukan marasa lafiya a ko-ina a fadin jihar domin shirin ko ta kwana.

 

 

Udom ya kara da cewa gwamnati za ta ci gaba da wayar da kan mutanen jihar hanyoyin kiyaye kai yadda za kiyaye daga kamuwa daga cutar.© hutudole

Post a comment

 
Top