Wannan shafi na hutudole a madadin shugaban shafin muna amfani da wannan dama wajan tunatar da kawunan mu cewa mafuta daya ce shine musulmai su koma ga Allah, su kuma nemi tsarin shi, domin babu mai iko sama da Allah ma haliccin mu.

Dafarko musani ita addu’a tana da laddubanta muddin kanaso Allah ya amshi addu’arka, dole ne ka tsarkake niyyar ka, kasani babu mai iko sama da Allah kuma shine kadai zai iya kare ka daga duk wani abun dakake tsoro.

Yana dakyau ka lazimci karanta wannan addu’a bayan kowacce sallar farillah domin neman tsarin Allah daga wannan Annoba ta COVID-19.

ALLAHUMMA INNI AUDHUBIKA MINAL BARSI, WAL JUNOONI, WALJUZAAMI, WA MIN SAYYIL ASQAAM

Baya ga haka yana da kyau kayi amfani da shawarwarin likitoci da suka bayyana kuma ka bisu domin hakan babu laifi, sabuda Addinin Musulunci “wayayyan Addinine “© Abubakar Saddiq

Post a comment

 
Top