A irin tataburzar dake faruwa a ‘yan kwanakin nan tsakanin shugaban hukumar tace fina-finai na jihar Kano Alhaji Isma’ila Na’abba Afakallahu da kuma fitaccen jarumin barkwancin nan Baban Chinedu.
Lamarin dai ya samo asali ne lokacin da fitaccen jarumin ya bayyana a wani bidiyo yake kalubalantar shugaban hukumar akan kayan auren ‘yar gidan marigayi Rabilu Musa Ibro da aka bayyana cewa an bayar.
Jarumin ya ce babu wannan maganar, domin kuwa su basu ji ba kuma basu gani ba. Dalilin hakane ya sanya mutane da yawa suka yo caa akan jarumin inda suke bayyana cewa sai babatu yake yi kullum amma har yanzu ya kasa gabatar da shaida.
Jarumin ya ce bai so yayi magana ba, yaso ya bari komai sai anje kotu tukunna zai gabatar da shaidar tashi, to amma dalilin maganganun mutane ya sanya ya fito da wata shaida guda daya ya bayyanawa mutane.
Jarumin ya bayyana a wani sabon bidiyo dauke da wata mujallar fim da aka buga a shekarar 2018, wato a lokacin da aka gabatar da bikin diyar Ibron, ya karanta dalla-dalla abin da aka rubuta a jikin mujallar wanda yake da nasaba da daukar nauyin auren da gwamnatin jihar tayi a jikin mujallar.
Ga dai bidiyon abinda jarumin ya bayyana:To bayan wannan bidiyon kuma, akwai kani a wajen marigayi Rabilu Musa Ibro da ya bayyana cewa shi ma dai yanzu shekara biyu kenan, bai san da wani zancen kayan aure ko kuma kudin kayan aure da gwamnati tace ta bayar na bikin diyar Ibron ba.


©HausaLoaded

Post a comment

 
Top