Bayan da labarai suka watsu cewa tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango zai kara aure wanda za'a daura a ranar 3 ga watan Mayu, Adamun ya fito yace an dage auren nasa sai bayan Sallah.

A sanarwar da ya fitar ta shafinshi na Instagram, Adamu ya bayyana cewa, an dage auren nashi har sai bayan Sallah kuma zai sanar da sabuwar ranar auren nashi nan gaba.

Post a comment

 
Top